Limamin Masallacin dake Titin Maiduguri Road Malam Muhammad Bin Uthman shine yayi wannan Kira a yayin Hudubar babbar sallah a yau.

Bin Uthman Wanda a cikin Hudubar sa yayi Kira da mawadata dasu sanya Farin ciki a zuciyoyin Marayu, da mabukata ta hanyar ciyar dasu a wannan lokaci da ake Farin ciki.

Ya kuma yi Kira ga shugabanni da su tabbatar da samar da tsaro da kuma ababen more rayuwa musamman ruwa saboda wannan lokaci ana bukatar ruwa don gudanar da ayyukan nama da tsaftace wuraren da akayi fidan raguna da shanu a wurin.

Daga karshe ya jiddada kiransa Al’umma da su ji tsoron Allah a wannan lokacin bukukuwa ta hanyar ziyarar wuraren da basu dace ba, musamman mata.
Haka zalika yayi Kira da iyaye da su kula da Inda yayansu ke zuwa da kuma sa’ido akan wayanda suke ma’mala dasu Allah zai tambayi su akan kiwon da ya basu.

Ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya a jihar kano da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: