Shugabar Ma’aikatan Najeriya Uwar gida Winifred Oyo-ita ta musanta zargin da ake mata na batan kudade har nairan Biliyan 16 a ofishinta.

Kudin da ake zargi sun bata na Ma’aikatan da sukayi Inshoran lafiya ne.

Mis Oyo Ita ta musanta zargin ne a gaban Shugabannin gudanarwar dake bibiyan yadda Al’amuran ma’aikat ke gudana a birnin Abuja.

Jaridar Premium time ta rawaito cewa wata jarida ce ta yada labaran batan Kudin a Ofishinta.

Sai dai Shugabar ta jaddada musanta zargin a yayin zantawarta da manema labarai inda tace zance ne na karya Wanda bashi da Fushe bare makama,
Kuma Kazafi ne kawai ake mata, don bata mata suna a idon duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: