Wata gobara da tashi a wani gida dake Kauyen Abagbo a jihar legas yayi sanadiyar konewar Yara 5 kurmus.

Kakakin Rundunar yansandan jihar Legas Bala Elkana ya tabbatar faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai inda yace Yara 5 ne suka suka rasa ransu sakamakon gobarar da ta tashi a cikin gidan.

Elkana yace yaran an rufe su ne a cikin gida ba tare da barin wani babba a cikin su ba Wanda zai kai musu agaji a lokacin da wani abu ya faru.

Yaran da suka kone sun hada da Folake Ogundaya, Abigail Ogundaya, sai Daniel da Bakare, sauran sun hada da Nmamdi da Khadijat.

Har zuwa yanzu ba’a San musabbabin tashin gobarar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: