A cigaba da gudanar da hada hada bukukuwan sallah a yankin Kashmir.

mahukuntar India sun baza jami’an tsaro don gudun barkewar Rigima saboda matakin da India ta dauka na soke kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin kan yankin kashmir Wanda mafi yawan Al’ummar Yankin musulmai ne.
hakazalika mahukunta sun katse wayoyin sadarwa a yankin baki daya.
A yanzu haka jami’an tsaro na gudanar da sintiri a garin Srinagar da kuma sauran manyan birane da ke yankin Kashmir.
sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa firaiministan Pakistan Imran Khan, ya bayyana matakin da India ta dauka kan Kashmir a matsayin mamaye wadda ba ta da bambanci da wadda ‘yan Nazi suka yi a lokacin yakin duniya na biyu.

Photo RFI
