Mahukuntar Kasar Saudiyya,sun Amince da amfani da harshen Hausa wajen gabatar da tunatarwa.
Haka zalika Hukumomin sun zabi Dakta Magaji Falalu Zarewa, a matsayin Wanda zai rika gabatar da karatuttuka da kuma tunatarwa a cikin wannan Masallaci mai albarka.
Har ila yau, wannan majiyarmu ta Muryar yanci ta ruwaito cewa, Hukumomin sun tsayar da lokacin bayan sallar Magariba da kuma Sallar Isha’i na kowace rana, a matsayin lokacin da Malam Zarewa, zai rika gudanar da wannan karatu nasa da kuma gabatar da tunatarwa ga dimbin al’ummar Hausawa da sauran masu jin yaren Hausa daga kasashen duniya daban-daban.