Jarumin fina finan Hausa Adam Zangio ya bayyana ficewa daga ƙungiyar masu shirya fina finan Hausa Kannywood.

Hakan ya biyo bayan aike da wani darakta a masana antar gidan yari bisa zatrgin da hukumar ta masa na sakin wasu waƙoƙi ba bisa ƙa ida ba.
Sunusi oscar ya kasance mai bada umarni sannan kuma masoyin kwankwaso.

Mujallar Matashiya ta fahimci cewa ana alaƙanta aike da daraktan gidan yari da sa hannun Ali Nuhu wanda har yanzu bai ce komai a kai ba.

Baya ga Adam Zango da ya fice daga ƙungiyar shima jarumi Mustapha Naburaska ya bayyana ficeear daga ƙungiyar.
Masana antar kannywood ta kasance cikin tangal tangal tun bayan da zazzafar adawa ta fara ɓilla tsakanin ɓangaren mabiya jam iyyar PDP da APC.