Najeriya Za Ta Tarwatse Kuma yan Arewa Ne Za Su Sha Wahala wannan kalaman fitaccen Malamin Addinin musulunci kenan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi.
Inda ya ja hankulan shugabannin Arewa akan cewar kasar nan ka iya rabuwa gida biyu kuma yankin arewa ne za su fi shan wahala.

Malamin ya ce rikici zai balle a arewa idan hakan ta faru yayin su kuwa yankin kudu za su yi kokari wajen daidaita yankunansu.
A cewarsa “Na ga matsala na tunkaro Najeriya, kuma hakan ba karamin illah zai yiwa yan Najeriya ba,” Gumi ya bayyanawa jaridar Sun. Ta majiyar mu Ta Al’ummata, cewa
“Bari na fada muku abinda zai faru da yankin arewa idan har kasar nan ta rabe gida biyu.
Yankin kudu maso yamma da yankin kudu maso gabas za su yi kokarin ganin sun daidaita yankunansu, yayin da yankin arewa zai kasance cikin rikici da tashin hankali.
Zamu fara tunanin ta yaya zamu kawo karshen Boko Haram dake yankin arewa maso gabas? Da kawo karshen matsalar fulani makiyaya a arewa? Ba zamu iya kawo karshensu ba. A cewar Gumi.
“Maganar gaskiya ma shi ne, kokarin da yankin kudu su ke yi wajen yakarsu shi ne yake rage musu karfi, amma idan suka tafi suka barmu da su na tabbata arewa ta gama lalacewa kenan.
“Kuma Najeriya za ta zama kamar kasar Lebanon ko Yemen. Babu wanda zai iya kawo karshen matsalar arewa tunda babu wani wanda yake da wannan karfin a arewa.
“Duk mutanen arewa kowa na nuna bangaranci na yare in da hakan ba karamin barazana bane ga kasar nan. Yankin kudu maso yamma suma sun rarrabu amma kuma su basu kaimu rikici ba.
Al’ummata/The Sun

