Hukumomin kasar Birtaniya sun yanke hukunci daurin shekara hudu a gidan yari kan wani matashi Dan Najeriya bisa kamashi da hodar Iblis a cikinsa.

Matashin mai suna Nwankwo mai shekaru 27 ya hadiye kullin hodar Iblis guda 67 a cikinsa Wanda akayi kiyasin darajarsa ta kai ta Euro Miliyan tamanin da biyu, da dari biyu da goma.
An kama Nwankwo ne a yunkurinsa na na tahowa birnin London daga kasar Brazil.

Nwankwo ya kasance mazaunin Birnin Peterborough ne dake gabashin ingila.

Rahotanni sun tabbatar ya tsallake kasar Brazil ba tare da an kamashi ba zuwa Birnin London anan ne aka gano yana dauke da da hodar Iblis a cikinsa bayan Na’ura ta tabbatar da hakan inda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari.