Wata kotu dake birnin Niamey a kasar Nijar ta yankewa wasu jami’an yansanda hukuncin daurin Shekara daya a gidan yari, sakamakon kamasu da laifin cin zarafin dalibin jami’a tare da dukanshi a lokacin da dalibai ke gudanar da zanga zanaga a birnin Niamey.

Kotun ta Kuma Umarci yan sandan da su biya Tarar kudi Cefa Miliyan 15 Wanda yayi kimanin Yuro 23,000 ga daliban da suka jikkata a lokacin zanga-zangar.
Kotun tayi La’akari da hujjan da ta samu ta wani faifan bidiyo da aka dauka a lokacin da ake gudanar da zanga-Zangar inda aka nuna yan sanda guda 3 na dukan dalibin da suka kama a bayan mota .
Kamar yadda Rfi ta rawaito.

