Connect with us

Labarai

Idan gwamnati ta ƙi magance damuwarmu, to da kanmu za mu ɗauki mataki

Published

on

Manoma kaji a jIhar Kano sun sha alwashin ɗaukar mataki muddin gwamnati ta ƙi magance matsalar da suke fuskanta.

Alhaji Muhammadu Aminu Adamu wanda mutane suka sani da Abba Boss ne ya bayyana hakan cikin wani shiri da aka yi da shi a mujallar Matashiya.

Abba Boss wanda shi ne shugaban kamfanin NANA FARM LTD ya ce akwai kamfanin da gwamnati ta bawa dama don yin sana a irin tasu alhali hakan zai zamto barazana ga masu ƙaramin ƙarfi.

“Hakan babbar illa ce kuma mabaraza ce ga tsaro duba ga mutanen da suke ta barin sana ar saboda ƙarancin kasuwa” Inji Abba Boss.

Ya ce kamfanin na ƙyan,ƙyasar kaji ya siyar musu daga baya kuma ya zo yana yin kwai sannan su siyar a farashi ƙasa da nasu kuma hakan ya saɓa ga dokar ƙasa.

Sannan ya yi kira dababbar Murya cewa ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki in kuma ba haka ba su da kansu za su ɗauki mataki.

“Da yawan manoma kaji na barin sana ar tasu saboda rashin ciniki da suke fuskanta”. Abba Boss.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

An Kone Ofishin Yan Sanda A Anambra

Published

on

Wasu ƴan daga sun kai hari tare da ƙone ofishin ƴan sanda a jihar Anambra.

 

An kai harin ne ofishin ƴan sanda na Neni da ke ƙaramar hukumar Anaocha a jihar da misalin ƙarfe 02:00am na dare wayewar yau Alhamis.

 

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Tochukwu Ikenga ya ce mutanen sun kai harin ne da abin fashewa da ake zargi bam ne.

 

Sannan ya ce maharan ba su ɗauki makaman jami’an ko yin garkuwa da jami’an su ba.

 

Ya ƙara da cewa, maharan sun gudu bayan da ƴan sanda su ka ci ƙarfinsu.

 

Zuwa yanzu ana ci gaba da hibiya don gano su waye su ka kai harin tare da kamasu.

 

Sai dai bai bayyana asarar da aka yi ba a sakamakon harin da aka kai.

 

 

Continue Reading

Labarai

An Kama Ƴan Fashin Da Su Ka Yi Wa Matar Aure Fyaɗe A Jigawa

Published

on

Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami haɗi da fyaɗe ga matar aure a jihar.

 

Kwamishinan ƴan sandan jihar AT Abdullahi ne ya bayyana haka yau Alhamis.

 

Ya ce an kama mutane uku bayan da su ka shiga gidan wani Mudan Ibrahim mazaunin ƙauyen Chori a ƙaramar hukumar Ringim tare da yi masa fashi daga bisani su ka yi wa matarsa fyaɗe.

 

Ƴan sandan sun samu labarin ne a ranar 17/03/2024.

 

Bayan zurfafa bincike, jami’an sun kama wani Umar Ibrahim, Umar Nasara, da wani Abubakar Isah dukkaninsu mazauna ƙauyen Chori a jihar.

 

Tuni aka ci gaba da zurfafa bincike a kai, kuma da zarar an kammala za su gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda kwamishinan ya shaida.

 

A wani labarin kuma kwamishinan ya bayyana nasarar kama wasu ƴan fashi da makami, da kuma wasu da ake zargi da aikata sata a jihar.

 

 

Continue Reading

Labarai

Malamin Makaramtar Firamare Na Kuriga Ya Mutu A Hannun Ƴan Bindiga Kafin Kuɓutar Da Dalibai

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya sha alwashin ɗaukar nauyin karatun ɗalibai 137 da aka kuɓutar daga hannun ƴan bindiga.

 

Ɗaliban su ne waɗanda aka yi garkuwa da ssu daga makarantar firamare ta Kuriga a jihar.

 

Gwamnan ya ce zai ɗauki nauyin karatun nasu ne daga matakin Firamare zuwa sakandire ƙarƙashin cibiyar Uba Sani Foundation.

 

Gwamnan ya bayyana haka yau Alhamis kafin mayar da ɗaliban zuwa Kuriga.

 

Ya ce bayan kuɓutar da su, an ɗauki lokaci domin duba lafiyarsu kafin miƙasu ga iyayensu.

 

Ya ce guda cikin malaman da aka yi garkuwa da su mai suna Malam Abubakar, ya rasa ransa a hannun ƴan bindigan.

 

A sakamakin haka, gwamnan ya ce zai ɗauki nauyin karatun ƴaƴan malamin, tare da bai wa iyalansa naira miliyan goma.

 

Akwai waɗanda su ka samu larurar kwakwalwa daga cikin ɗaliban da aka kuɓutar, a don haka su ka miƙasu ga kwararrun likitoci domin duba lafiyarsu.

 

Sannan gwamnatin ta bayar da umarnin yin wasu ayyuka a Kuriga, wamda gwamnan ya ce garin na daga cikin garuruwan da su ka fi zaman lafiya a jihar.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: