Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce abin alfahari ne kasancewar shugaban ma aikatan fadar gwamnatin Kano mutum ne nagartacce.

Gwamna Ganduje ya ya yi wannan furuci ne yayin da iyalan Alhaji Bukar Makoɗa suka kai masa ziyarar godiya bisa babbar kujera da ya miƙa gidansu.

Ya ce Alhaji Ali Haruna Makoɗa nagartacce ne mai asali a jihar nan kuma mai ilimin addini da zamani wanda duniya ta shaida hakan.

Dukkan jawabin na ƙunshe cikin sanarwar da baban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar a yau.

Ganduje ya sha alwashin aiki tuƙuru don cimma manufar samar da cigaba ingatacce a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: