Akalla yara Uku ne Ambaliyar Ruwa yayi awon gaba daau a unguwar saidawa dake karamar hukumar Dambatta a jihar kano.

Mai magana da yawun karamar hukumar Dambatta Nura Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin Inda ya tabbatar da cewa Mata Biyu ne suka rasu da namiji daya sune Ambaliyar Ruwan yayi awon gaba dasu sakamakon Ruwa Mai karfin gaske.

Nura ya Kuma kara da cewa Akalla unguwanni Hudu ne suka samu Asarar Dukiyoyi da Gidaje sakamakon karfin Ruwan, unguwannin sun hada da Fagwala, Makera, da Turu, sai Kuma Unguwar Mahuta.

Shima anasa jawabin A yayin da ke Mika tallafin Kayyayaki ga Wanda ifti’la’in ya afka musu, shugaban karamar hukumar Alh Musa Dambatta ya nuna damuwarsa da kuma tausaya musu bisa Asarar Dukiyoyi vda sukayi da rayuka.

A wani cigaban labarin Kuma hukumar kashe gobara ta jihar kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro Mai shekaru 12 mai suna Isma’il Safiyanu a cikin kududdufi a lokacin da yake wanka a Kuddudufin Unguwar sharada kwanar Mai jego.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar kano Alhaji Saidu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: