Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta bayyana cewa ta hada hannu da Ofishin Bincike na Kasar Amurka FBI don dakile masu damfara ta shafin yanar gizo.

EFCC tace tun bayan hada hannun da sukayi FBI yanzu haka sun kama matasa 16 a Abuja da laifin Damfara ta yanar gizo wanda aka fi sani da Yahoo Boys.
Shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin da yake karbar bakoncin shugabannin masana harkar yanar Gizo gizo a Ofishin say dake Abuja.

Magu ya kara da cewa idan sun gama Bincike zasu gurfanar dasu a gaban kuliya.
