mutanen da suke dauke cutar tabin hanakali zai karu nan da wasu shekaru talatin masu zuwa.
kamar dai yadda Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwar data fitar inda ta bayar da sababbin matakan da za’a bi wajen rage masu dauke cutar,ta hanyar basu magunguna.
“Babban Daraktan Hukumar lafiya ta duniya Tedros Ghebreyesus shine wanda ya bayyana hakan, a wani bayanin da ya yi aka kuma fitar da shi,inda ya ce, ‘Ya kamata mu yi dukkannin abinda ya kamata saboda a samu rage yiyuwar kamuwa da ita cutar ta tabin hankali.”

“Su dai bayanai na kimiyya wadanda aka samu wadanda kuma gamsassu ne sun bayyana cewar zuwa wani lokaci abinda yake kyau ga zuciyar mu, shima yana da kyau ga kwakwalwarmu.”

Kamar dai yadda su sharuddan suka bayyana mutane na iya kaucewa yiyuwar kamuwa da cutar tabin hankali ta hanyar yin motsa jiki, a kuma daina shan taba, sai kuma kauce ma babbar matsalar amfani da giya, da kuma shan kwayoyi musamman ga matasanmu.
Sauran sharuddan sun hada da kada a sake a kamu da kiba, sai kuma cin abinci wanda ya kunshi dukkannin abubuwan da suka kamata, ga kuma shi al’amarin daya shafi bugawar jini kamar dai yadda yadda jaridar Leadership ta Rawaito.
“jaridar ta kuma kara da cewa akwai mutane miliyan kusan 10 wadanda suke kamuwa da sababbin nau’oin ita cutar ko wacce shekara, abinda kuma yake samar da babbar matsalar da take damun al’ummar Najeriya musamman saboda yawaitan shaye shayen miyagun kwayoyi da matasa ke yi a yanzu.