Gwamnatin jihar kano ta ayyana Ranar litinin 2/satumba/2019 a matsayin Ranar hutu bisa murnar shiga sabon shekara na Addinin musulunci na shekarar 1441AH.

Wannan sako ya fito ne daga hukumar yada labarai da Al’adu na jihar kano wanda jami’an Hulda da jama’a Sani Abba yola ya sanyawa hannu.

Sanarwar ya bayyana cewa gwamnanan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Umarci Al’ummar jihar kano da suyi amfani da wannnan rana don yi wa jihar kano Addu’ar zaman lafiya da bunkasar arziki, dama kasa baki Daya.

Ganduje ya kuma taya daukacin Al’ummar jihar kano murnar shiga sabon shekarar musulunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: