Arewa da sauran gyara?
Babbar matsalar mu a Arewa shine rashin hadin Kai da rashin kishin junan mu, sai kuma matsalar aikin yi wacce ke Sawa matasan yankin, na yin ayari su nufi kudancin kasar domin ci rani, a wajen ci ranin ne suke gamuwa da wulakanci, kwatankwacin Wanda ya faru GA matasan Arewa su 123 a Ikko. Wannan abin haushi ne Wanda ke nuna cewar al’ummar Arewa sun zama saniyar ware, jagororin mu kuma Galibinsu idon su ya rufe basa hango komai sai abin da zasu samu su tarawa iyalansu dukiya. Muna gani kirkiri matasan mu na gararamba a Gari Amma an kasa hada Kai domin tunanin tartibiyar hanyar samar da makoma ga yankin. Wani abu dake damu na, shine duk da cewar matasan Arewa sune, suka fi yawa amma duk wani gurbin aiki da aka samu na bankuna, Kamfanoni masu Zaman kansu, ko kantunan zamani, sai ka iske ba matasan Arewa ake baiwa gurbin ba, alal misali, duk da yawan namu, kiri kiri za a samu gurbin aiki a Kano ko katsina, Amma idan kaje kaga ma aikatan sai kayi ta mamakin yadda aka dauki aikin domin yawanci wadanda ake baiwa ayyukan ba Yan Arewa bane, kaga kenan can sun cike nasu guraben ayyukan, na Arewan ma sunzo sun cike ko kuma an cike dasu. Wai meye matsalar ne? Hatta aikin gadi a manyan kantunan zamani (shopping malls) indai na Yan kasashen waje ne, zaka tarar mutanen Arewa kalilan ne, to shin matasan mu ne basa aikin ko kuwa jagororin mu ne basu da kishin mu? Nasan dai ko aikin gadi aka samu a yanzu a Kano ko katsina da sauran su akwai dimbin matasan mu da zasu yi rige rigen karba, domin nasan matasan dake da digiri da diploma ko NCE da suka yi karatun zama masu gadi kuma suke aikin gadin a yanzu,amma zai yi wuya ka gansu a irin wadannan wurare suna gadin, to Wai meye laifin su? Wani abu da nake mamakin sa shine yadda abin ya Sha bambam a kudancin Nigeria, domin zai yi wuya a Bude shop rite ko Grand square da sauran irinsu a Lagos ko Enugu kuma kaga Galiban ma’aikatansu mutanen Arewa ne,sai dai a Arewa, saboda muna da Karancin masu kishi wadanda zasu tsaya tsayin daka domin ganin an yi adalci kowa an bashi hakkin sa, Da zamu yi, yadda ake a kudu da watakila mun rage yawan matasa masu gararamba a Gari, Yawanci wakilan mu da jagororin mu, sun fi son fafa, da birgewa kaga mutum Dan tsigigi bashi da ko dubu 50 cikakkiya Amma da an zabe shi ya samu dama sai kaga yana ta sayen gidaje a GRA da manyan motoci ya sauya mu’amilla yayi ta sharholiya domin a zatonsa ya Sha kwana, Ya manta da irin wadannan matasa wadanda watakila ma sune suka taimaka wajen tsare masa akwatu.Ya kamata mu farka mu gane cewar zamani fa sauyawa yake, Kuma baka da inda yafi yankin ka, idan takamar ka, ka riga kasha kwana ne, to fa akwai sauran aiki a gaba. Allah ya maganta mana, ya saita mana shugabannin mu ya saita su akan hanyar daidai. Allah ya kawo mana tallafi ya ceto mu daga fadawa ramin da muke tunkara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: