Gwamnatin jihar zamfara ta bayyana cewa zata shigar da yaren fulatanci cikin tsarin koyarwa a makarantun jihar, a kokarinta na fara aikin Gina Rugage da Mai girman Hekta 300 a fadin jihar.

Gwamnan jihar Bello Matawalle shine ya bayyana haka a garin Gusau a lokacin da yake karbar bakoncin masu bada shawara kan yadda Taswirar Shirin Gina Rugagen zai Kasance.

A cewar gwamnan yaren fulatanci yare ne da yayi fice a wasa Kasashen Afrika a kalla kasashe 20 na yammacin afrika.

Gwamnan ya kuma bawa hukumar Ilimi na jihar umarnin fara aikin shigar da yaren cikin tsarin koyarwa Wanda hakan zai taimaka wajen amfani da yaren musamman ga yara masu tasowa.

Ya kuma kara da cewa yaren fulani na bata kasancewar ba’a raya shi don haka gwamnan ya bukaci a saka yaren a tsarin koyarwa don farfado da yaren ganin yadda bata a bakunan Al’ummar fulanin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: