Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Mu shaƙata

Mawakiya Queen Zeeshaq ta kalubalanci makarantun kasar nan kan rashin samar da darasin Soyayya

INA KALUBALANTAR KWALEJI DA JAMI’O’IN KASAR NAN KAN SOYAYYA

Gaskiya na Kalubalanci jami’o’i da kwalejin kasar nan,, bisa rashin samar da courses kan abin da ya shafi SOYAYYA.

Idan har soyayya tana da muhimmanci ya kamata a sa ta cikin jadawalin karatuttukan makarantu, tun daga tushe.

Ta yadda zaa ke kowa zai iya ta ba tare da an samu tangarda ta yaudara ko yawo da hankali a tsakanin masoya ba.

Na ga dai akwai courses wadanda har rayuwar aure suke koyawa kamar: Family life and emerging health issues (FLEHI), kuma dukkan Wanda ya karanta course din yasan me ke qunshe dashi, babu wata kafa ta yadda ake sarrafa auratayya da baai magana a ciki ba.

A sanina, dole sai anyi soyayya tukun ake aure,, to me yasa ba zaa fara koya soyayyar ba, sae a tsallaka rayuwar aure??

Daktocin mu, da farfesoshin mu,,, da malaman mu, da kangaran din mu, duk sun san gudunmawar da soyayya ke badawa a tsakanin alaumma, sun san cewa idan ta gyaru raywuar matasan mu zata gyaru idan ta baci to fa sae ta shafi kowa.

Ba wai don ina soyayya ko zan yi soyayya yasa nai wannan batu ba aa naga kullum ita ce matsalar jama’ar mu, sae nake ganin kamar rashin sanin yinta yadda ya dace ne yake kawo hakka,, amma da ace zaa santa a ilmance aka karanta ta,, to zaa samu rangwame.

Ya kamata a duba!!!!

Queenzeeshaq
2/9/2019M
3/1/1441HA

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: