Wasu mutane da ake zargin yaran Dan Majalisar jihar kano ne Mai wakilatar Karamar hukumar Minjibir Tasi’u Ibrahim Zabainawa Sun lakadawa wani dan Jarida duka a lokacin da yake gudanar da aikin sa.
Dan jaridar Mai suna Sani Abdurrazak Darma ma’aikacin Gidan Rediyon Express ne dake jihar kano.
Ya gamu da fushin yan garin ne a lokacin da yake gudanar da tambayoyi kan yadda suke Ribatar ayyukan da Gwamnati take musu ta cikin Shirin Express a Karkara.
Anan ne aka samu wasu matasa inda suka nuna basu yadda a rika tambayarsu ba game da ayyukan da ake musu saboda idan aka sa A Rediyo Baza’a cigaba da yi musu aikin da aka fara ba.
Sai dai wata majiya sun bayyana cewa Dan Majalisar jiha na Karamar hukumar Minjibir Tasi’u Ibrahim Zabainawa yayi wa wasu Daga cikinsu Alkawarin Basu takardar daukar aiki wato( Offer) shine dalilin da yasa basa son ayi tambaya kan aikin da yake yi a Karamar hukumar.
Sai dai hukumar Gidan Rediyon Express din ta nemi jin ta Bakin Dan Majalisar akan faruwar lamarin sai dai yace su saurareshi kasancewar bai dade da dawowa daga aikin hajji ba.