Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN tayi Kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da ya dakatar da kungiyar fulani ta Miyetti Allah Don tinkarar yaki da masu garkuwa da mutane a fadin Najeriya.
Haka zalika kungiyar ta CAN to tayi Kira da Shugaban kasa da ya dakatar da Shirin Gina Rugage a fadin Najeriya .
Kungiyar tayi wannan Kira ne ta Bakin Shugaban kungiyar Samson Ayokunle.
Inda yayi wannan Kira ne a Taron da suka gudanar a jihar legas biyo bayan kwamitin da aka kafa kan tabbatar da Shirin Gwamnatin Tarayya na Gina Rugage.