‘Yansanda sun nemi KAROTA ta mika musu ma’aikatan da suka yiwa direba jina-jina

A yammacin yau Talata ne dai aka samu barkewa rikici tsakanin ‘yan KAROTA da direbobi Tirela sakamakon fasawa daya daga direbobin kai da jami’an hukumar Karotan sukayi, akan titin Ibrahim Taiwo Road, dake nan Kano, kamar yadda daya daga cikin direbobin mai suna Auwal Yusuf ya shaidawa Mujallar Matashiya a yayin da ake tsaka da dambarwar, shima direban mai suna Abdulkarim Muhammad wanda cikin jini jabe-jabe ya shaida mana cewa ‘yan Karota ne suka yi masa wannan aika-aika ta hanyar duka da gora, ya kuma yi fatan mahukunta zasu bi masa hakkinsa.
Mujallar Matashiya tayi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar ta KAROTA wato Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa amma abin yaci tura.

Kalli Hoton Yadda Direbobin Tirela Suka Rufe Hanya Kafin ‘Yansanda Su Shiga Tsakani

Shima a nasa bangaren kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Kano, DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana mana cewa rundunarsu bata yi kasa a gwiwa ba a lokacin da ta samu labarin ta hanzarta zuwa wajen kuma tuni suka kai direban zuwa asibiti sannan, sun nemi hukumar KAROTA data mika su ma’aikatan da sukayi aiki a wurin a yau.
Allah ya kyauta.