Connect with us

Labarai

Ra’ayi: Iran, Saudia Sun Kama Hanyar Rusa Arewa -Sharfadi

Published

on

Iran, Saudia Sun Kama Hanyar Rusa Arewa

Babu shakka ga duk mai bibiyar irin muhawarori da ake tafkawa a kafofin sada zumunta na zamani, musamman a nan Arewacin Najeriya zai fahimci yadda ake zazzafar kazamar muhawara a tsakanin manyan bangarori biyu wanda idan ka bisu a hankali sai ka fahimci duka tushen da suka tsiro yana tikewa ne ga turbar siyasa ta kasashen Saudi Arabia da kuma kasar Iran, yana da matukar wahala mutum ya iya fahimtar hakan a lokaci guda, kasancewar yadda siyasar wadannan kasashe tayi tasiri da sunan addini, wanda mu kuma a Arewa duk abinda aka jinginashi da addini zai wuya jama’a su fahimci illarsa.

Matasa sune ke nuna halin da al’umma zata kasance a gaba, kafin wannan rubutun na bibiyi zauruka da dama musamman a Facebook da kuma WhatsApp wadda na ganewa idona yadda matasa da dama tunaninsu ya juye matuka, daga tunanin kawowa al’ummar mu cigaba, zuwa tunanin kare muradun siyasar wadannan kasashe, wanda dukkansu siyasa ce suke sai dai kawai wasu sunfi wasu iya taku.

Kasancewar da yawa daga matasan mu basu da ‘yancin yin tunani sai-dai ayi musu, wanda zaku fahimci hakan a kwanakin baya lokacin da akace wata mawakiya zataje kasar Saudi Arabia don gudanar da wasanta na nishadi, wanda bai da alaka da musulunci, tunda ba da sunan musulunci tace zataje ba, sai gashi masu bin siyasar kasar suna kokarin baiwa zuwan nata kariya da sunan larura ce, su kuma masu bin siyasar Iran suka fara sukarsu ta ko ina, ba wai don sun sabawa musulunci ba, sai don kawai a ga wallen kasar da ta sabawa kasar Iran.

Irin hakan ta faru a kwankin baya lokacin da alaka tayi tsamari, tsakanin kasar Iran da Amurka wadda ko kadan ba rigima ce ta addini ba, amma sai gashi masu goyon bayan siyasar Saudi Arabia suna goyon bayan Amurka, su kuma masu goyon bayan siyasar Iran suna goyon bayanta.

Shekaran jiya ina jin karatun Dr. Ahmad BUK a rediyo, sai naji yana bada labarin wasu shekaru a baya da kasata Najeriya tafi kasashen Saudi, Dubai da sauransu cigaba, wanda a yanzu ba haka abin yake ba.

Tabbas akwai bukatar matasan mu, su fahimci cewa maida hankali wajen siyasar wadancan kasashe, maimakon maida hankali kan cigaban kasarmu babu wani abu da zai tsinana mana sai koma baya.

Zan dakata a nan, don gudun tsawaitawa.

Basheer Sharfadi
04-09-2019.
#NigeriaFirst #Nigeria #SaudiArabia #Iran

1 Comment

1 Comment

 1. Haruna Dan umma7

  September 5, 2019 at 11:08 am

  Ni banaganin cewa wannan dalili ne Na cewa saudiya da Iran sun kama rusa arewa

  Domin rubutun da kayi ma baida alaka da kokarin wargaza arewa

  Wadanda suke sukan Zuwan mawaqiya suna suka ne saboda ganin girman Kasar aduniyar Musulunci, koda kuwa ita saudiya tana yiwa abun kallon shiyasa ne

  Kaga kenan mu ga kallon da mukeyi suma ga ganin da sukeyi, sannan kaima Sharfadi kasan kokarin bata tarbiyar musulmai da duniya takeson yi, kaga kenan ganin shiyasa baikamata ya hanamu hango Addinin mu ba

  Allah ya datar damu

Leave a Reply

Labarai

Kasar Dubai Ta Cirewa Najeriya Takunkumin Da Ta Sanya Mata

Published

on

Ministan yaɗa labarai a Najeriya Mohammed Idris ya ce ƙasar Dubai ta dage takunkumin da ta kakabawa yan Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin ganawa da yan jarida yau a Abuja.

Ya ce an cimma matsaaya kuma tuni hadaddiyar daular larabawa UAE ta dage haramcin bayar da biza ga yan Najeriya.

Ya ce daga yau Litinin yan Najeriya na iya tafiyar ƙasar ta Dubai.

Duk da cewar ministan bai bayyana cikakken bayani a kan haka ba, amma ya ce kowanne lokaci daga yanzu yan Najeriya na iya tafiya kasar.

Tun a baya dai gwamnatin Najeriya ke ta cuku cuku don ganin an dage haramcin bizar ga yan ƙasar waɗanda aka haramtawa zuwa.

Hadaddiyar daular larabawa dai ta kakabawa yan Najeriya takunkumin hanasu shiga tun a watan Disaamban shekarar 2021.

Dubai ta haramtawa ƴan kasashen Najeriya da Congo shiga kasar.

Continue Reading

Labarai

‘Yan Sanda A Kaduna Sun Haramtawa ‘Yan Shi’a Yin Taro A Jihar

Published

on

Rundunar yan sanda ajihar Kaduna ta haramtawa mabiya mazahabar Shia gudanar da kowanne taro a jihar.

Hakna na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun yan sandan jihar Mansir Hassan ya saanyawa hannu.

Ya ce rundunar ta haramtawa mabiya mazahabar ta Shia taron Ashura a shekarar da mu ke ciki.

Haka kuma yan sandan sun gargadesu kan su kaucewa yunkurin shirya kowanne irin taro

Sun dauki matakin haka ne ganin yadda aka samu asarar dukiya da raunata wasu har ma da rasa rayuka a tarukan da su ka yi a baya.

Sannan yan sandan sun hana yan Shia gudanar da kowacce irin zanga-zanga da kuma wani gangami da sunan Ashura a bana.

Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba.

Continue Reading

Labarai

Kotu A Kano Ta Hana Aminu Ado Bayero Da Sauran Sarakuna Hudu Bayyana Kansu A Matsayin Sarakunan Kano

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan Gaya, Karaye, Bichi da Rano amsa kansu a matsayin sarakunan Kano

Kotun ƙarƙashin mai shari’a Jusctice Amina Aliyu ta haramta haakan ne a zamanta na yau bayan da gwamnatin jihar Kano da majalisar dokoki ta jihar da shugaban majalisar da ma kwamishinan shari’a su ka shigar da kara a gabanta tun a watan Maris.

Kotun kuma ta umarci sarakunan da su mayar da dukkanin kaya mallakin gwamnatin jihar Kano

Kafin zaman kotun na yau, lauyoyin waɗanda gwamnatin ke ƙara sun bukaci kotun ta dakatar da shari’ar ganin yadda su ka daukaka kara

Sai dai alkaliyar kotun ta ki amincewa da bukatarsu ganin cewar ba ta samu umarni daga kotun daukaka kara ba.

Haka zalika, sun mika rokon soke sabuwar dokar da majalisar dokoki ta jihar Kano ta shigar amma kotun ta ki aminta, a cewar kotun ba a gabatar mata da gamsassun hujjojin da za ta ƙi aminta da sabuwar dokar majalisar ba.

A zaman da kotun ta yi ranar 4 ga watan Yulin da mu ke ciki ne dai lauyoyin da ke kare Alhaji Aminu Ado Bayero a gaban kotun su ka janye daga kare shi a shari’ar.

Gwamnatin jihar Kano ce dai ta shigar daa kara a gaban kotun ta na mai rokon kotun ta hana Alhaji Aminu Ado Bayero, da sarakunan Gaya Karaye Bichi da Rano amsa kansu a matsayin sarakunan Kano.

Tirkatirkar dai ta fara ne tun baya daa majalisar dokoki ta jihar Kano ta soke dokar karin masarautu tare da dawo a tsohuwar dokar da ta dawo da Malam Muhammadu Sanusi ll a matsayin sarkin Kano.

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: