Yau Shekara Daya da Komawar Shekarau APC

Malam Dr. Ibrahim Shekarau wanda tsoho malamin makranta ne wanda yayi gwamna har hawa biyu, wato tsawon shekaru takwas a Kano, karkashin jam’iyyar ANPP, Mallam Shekarau ya zama gwamna karo na farko a shekarar 2003 bayan da ya kada gwamna mai mulki Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda kuma Engr. Kwankwaso ya kara karbar mulki daga hannun Mallam Shekarau bayan da ya kammala zangon mulkinsa na biyu, ya kuma tsayar da danle lensa a takara wato Malam Salihu Sagir Takai.

Tsawon wannan lokaci ana ta tafka adawa kala-kala tsakanin manyan gidajen siyasar Kano wato gidan Mallam Shekarau da kuma gidan Engr. Kwankwaso.

Juyin juya halin siyasa da aka samar musamman na hadin kan jam’iyyun adawa wanda aka faro daga jam’iyyar CPC har zuwa APC mai lakabin MAJA wadda shugaban kasa na yanzu Mallam Muhammadu Buhari ya jagoranta sai ta sanya Mallam Shekarau ya tsinci kansa a jam’iyyar APC wanda ya zamo daya daga cikin manyan jiga-jigai da suka kafa jam’iyyar.
Sai dai a ranar wata Laraba ta watan Janairu na shekarar 2014 lokacin da zaben shekara ta 2015 ke kara karatowa Mallam Shekarau ya yanke shawarar barin jam’iyyar APC inda ya koma jam’iyyar PDP, wadda ake kallon hakan ya biyo bayan kome da Engr. Kwankwaso yayi zuwa jam’iyyar da su Shekarau suka kafa wato APC kuma ya shigo da gwamnati sukutum wanda hakan ya sanya ya kwacewa Mallam Shekarau madafun iko a jam’iyyar.
Shugaban kasa a wancan lokaci Good luck Jonathan ya karbi Mallam Shekarau hannu bibiyu harma ya bashi mukamin ministan ilimi na tarayyar Nigeria.
Kwankwaso ya cigaba da jagorantar jam’iyyar APC a Kano inda shima ya tsayar da mataimakinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dan takarar gwamna a zaben shekarar 2015 a yayinda shi kuma Malam Shekarau ya kara tsayar da Mallam Salihu Sagir Takai a jam’iyyar PDP.
Jam’iyyar APC ita ta lashe wannan zabe na 2015 daga gwamna har zuwa shugaban kasa, inda shi kuma Kwankwaso ya nemi Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya kuma yayi nasara a zaben, haka aka yi tafiya.
Rigima ta barke tsakanin Kwankwaso da kuma gwamna mai mulki Ganduje wadda har ta tilastawa Kwankwaso ficewa daga jam’iyyar APC inda ya sake komawa jam’iyyarsa ta asali wato PDP, inda aka kara mai-maita irin abinda ya faru a APC a 2014 inda Kwankwaso ya kara kwace madafun ikon jam’iyya daga hannun Mallam Shekarau, hakan kuwa shine ya sake tilastawa Mallam Shekarau din ya bar jam’iyyar ya dawo jam’iyya mai mulki ta APC a irin wannan rana ta 4 ga Satumban shekarar 2018, inda ya hada kai da gwamna mai ci Ganduje.
Jam’iyyar APC a Kano ta tsayar da Mallam Shekarau matsayin sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya wato mukamin da Engr. Kwankwaso ke kai a wancan lokacin, inda a gefe guda gwamna Ganduje ya sake neman zagaye na biyu, Kwankwaso kuma ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna.
A wannan zabe Shekarau ya lashe kujerar sanata wadda yake kai a yanzu, Ganduje ya koma kujerar gwamna, wadda har yanzu ake gaban kotu tsakaninsu da tsagin Kwankwaso wanda basu gamsu da sakamakon zaben ba.
Wannan sune kadan daga wasu batutuwa da suka faru a siyasar Kano wadda hausawa ke cewa sai Kano.
Sharhi: Basheer Sharfadi