Rundunar ƴan sandan jihar Naija ta kama wani soja bisa zargin kashe wani mutumin ta hanyar caka masa wuƙa.

Kwamishinan ƴan sandan jihar AlhajiAdamu Usman ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jihar.

Ya ce sojan mai suna Ashiru Jibrin ya cakawa wani muytumi wuƙa a kasuwar Lambatta a ƙaramar hukumar Gurara da ke jihar.

Kwamishinan ya ce sun sanar da jami an soji na jihar daga bisani kuma suka yi awon gaba da wanda ake zargin don zurfafa bincike.

Sai dai sojan na iƙirarin cewa ya yi yaƙi da ƴan ta adda a jihar Borno a cewar kwamishininan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: