Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Kungiyar Daliban kofar Mata sun tallafawa marayu Akalla 40 da kayan makaranta da littatafai a fadin Unguwar

Kungiyar Daliban kofar Mata dake Kano (KOSA) sunyi rabon kayan makaranta ga Marayu kimanin 40 dake unguwar.

Wannan dai bashi bane karo na farko da kungiyar ke wannan aikin na tallafawa Marayu ta fanni daban daban musamman wajen Ganin sun samu Ilimi kamar yadda Shugaban kungiyar kwamared Suleman Aminu Sule ya bayyana.

Inda yace akwai dalibai Marayu da suka dauki nauyin karatunsu na boko da na islamiyya karkashin kungiyar su, gashi yanzu sun tallafa musu da kayan makaranta da littatafai da sauransu.

Shima da yake jawabi a wurin taron mai unguwar kofar Mata Abba Muhammad Jibril yace abin da wayannan matasa ke yi shine abin da zai taimakawa marayun don rage radadin rashin iyayensu suji cewa su ma dai dai suke da sauran yara.

Kasancewar Ilimi shine gishin Rayuwa wannan kungiya sun San amfanin ilimi shiyasa suke wannan yunkuri na ganin sun tallafawa yara musamman Marayu a fannin ilimi.

Daga bisani daya daga cikin Iyayen kungiya Alh Sani Abdullahi kofar Mata yace abin wannan kungiya ke yi kalubale ne gare su dama duk wani mai arziki da masu fada aji a fadin jihar kano.

Don haka zasu cigaba da bada gudunmawa don ganin an cigaba da gudanar wannan aiki na tallafawa marayun Unguwar.

1 COMMENTS

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: