A daidai lokacin da ake tunanin mabiya mazahabar shi a za su fito don yin gangamin zagayen Ashura, Rundunar ƴan sanda reshen jihar kano ta ƙara jaddada hana wani taro ko gangami na ƙungiya ko siyasa a faɗin jihar.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Ahmed Ilyasu ya fitar wadda ke sanye da sa hannun mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna.

Rundunar ta ce ta haramta dukkan wani zagaye ko na ƙungiyar addini ne matuƙar ba ta bada dama ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa hakan ya biyo bayan samun bakin.zare a kan harkar tsaro wanda rundunar ta ce ƙoƙarin da ta ke a yanzu shi ne tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Sannan ta jakunnen mutane masu kunnen ƙashi da su yi kuka da kansu muddin suka bijirewa wannan umarni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: