Yadda Aka Karke Tsakanin Muneerat Abdussalam da Datti Assalafy a Karshe

Muneerat Abdussalam wata matashiya ce ‘yar soshiyal midiya wadda ke amfani da shafukan wajen zantar da kalamai irin na ma’aurata, inda daga bisani kuma ta kara bunkasa harkarta ta hanyar talla da kuma sayar da magungunan ma’aurata da sauransu, Muneerat ta faro harkarta ne ta shafin Instagram inda take da mabiya sama da dubu 30 wanda daga bisani kuma ta gangara shafin YouTube wanda take da mabiya sama da dubu 77 a halin yanzu, sai kuma Facebook wanda har yanzu rarrafe take.
Wani sashi na al’ummar Arewa dake amfani da shafukan soshiyal midiya na kallon Muneerat matsayin wata fitinanniya wadda take aikata ayyukan alfasha, inda sashen ke ganin ta riga ta kaucewa hanya da tsari irin na addinin malam bahaushe, yayinda a gefe guda wasu ke kallon tana da hurumin tayi abinda taso tunda dai kasa ce muke wadda bata addini guda ba, hassalima wasu na kallon abinda take tamkar wata hanyace ta gyaran aure.

Datti Assalafy yayi suna kwarai a shafin Facebook inda yake da mabiya sama da dubu 100 a yanzu, An sanshi wajen nuna kishin Arewa da kuma Addini, Datti ya kan tofa albarkacin bakinsa akan duk wasu abubuwa dake faruwa, misali ya shiga batun siyasar Kano a zaben 2019 yayi kace-kace, a lokacin da Kwankwaso yana APC yana cikin masu yabonsa, amma bayan ya bar APC ya sauya zuwa sukansa, haka ma Sarkin Kano, a baya yana yabonsa daga baya kuma ya juya, haka a baya yana sukar Mallam Shekarau daga baya kuma ya sauya, haka nan batun da ya shafi batutuwan ban-bance ban-bance dake tsakanin addini, sai dai a yayin da wasu ke kallon Datti matsayin dan rajin kare Arewa ko Addini, wasu kuma na yi masa kallon duk abinda yake yi matsayin kasuwace kawai irin ta bukata.

A farkon shekarar nan ne akayi wata dambarwa bayan da Datti yayi martani ga Muneerat wanda har ta bayyana cewa ya kafirta ta, ya kuma halatta jininta, wanda tayi ikrarin hakan ya jefa rayuwarta cikin hadari domin kuwa wasu sun nemi hallakata, inda ta sanarwa duniya cewa idan aka tsinci gawarta to babu shakka sanadiyyar Datti ne, mutane da dama sunyi tsokaci a soshiyal midiya kan wannan batu, sai dai ana tsaka da wannan dambarwa Muneerat ta tafi babban masallacin kasa dake Abuja inda ta sabunta kalmar shahada ta karbi musulunci a zagaye na biyu, bayan da ta bayyana cewa abinda ya faru tsakaninta da Datti yasa tayi fushi, har ta fice ma daga musulunci, bayan musayar muhawarori da aka dingayi a tsakaninsu ta hanyar wallafa bayanan martani ga kowa, Muneerat ta fito tayi Bidiyo wanda ta bayyana cewa tana kaunar Datti Assalafy kuma zata aureshi.
Batune Aure da Muneerat tayi kawai sai aka ga Datti ya dakatar da yin tsokaci ko martani a gareta, haka akayi wannan rikici, wadanda basu san Muneerat ba sanadiyyar wannan batu suka samu saninta, Muneerat ta bayyana cewa ta samu koma baya daga masu bibiyarta, ka sancewar ta koma yin bidiyo cikin hijabi ko kuma rufe jiki, sai dai rashin samun karbuwa da tayi ya sanya Muneerat ta sake komawa yadda ta saba yin bidiyonta wanda hakan ya kara bunkasa ayyukanta a soshiyal midiya.
Shin ko yaya batun soyayyarsu da Datti Assalafy?
Bayan da aka samu wata dambarwa a Facebook har ta kai an bayyana hotunan sa, kwatsam sai Muneerat ta fito ta bayyanawa duniyar rushewar soyayyar da tayi masa ta dan lokaci.
Shin ko akwai wani cigaba ko nasara da wani bangare ya cimma a tsakanin wannan dambarwa ta Datti da Muneerat?
Mai karatu na bar maka wannan amsa ka amsata azuciyarka.
Mujallar Matashiya
10-09-2019.