Inganta rayuwar matasa ta hanyar basu sana’io daban daban shine burin mu.

Shugaban Mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ne ya bayyana hakan ne a yayi da shugabannin kungiyar Daliban Kofar mata suka kawo ziyara ta musamman Ofishin mujallar matashiya a yammacin yau.

Ya Kuma kara da cewa zasu bada gudunmawar su ka kungiyar a duk lokacin da bukatar haka ta taso, don Ganin kungiyar ta cimma abin da tasa gaba.

Shima ana sa jawabin Shugaban kungiyar Daliban kofar Mata kwamared Suleman Aminu Sule ya bayyana makasudin kawo ziyara Ofishin mujallar matashiya don nuna godiya ta musamman ga Mujallar matashiya saboda irin gudunmawar ta ke bawa kungiyar ta fannoni daban daban.
Musamman a lokacin da take gudanar da Al’amuran a na tallafawa marayun kofar Mata.
Da kuma kulla alaka a tsakanin juna.

Daga karshe dai Shugaban mujallar matashiya Abubkar Murtala Ibrahim ya bada gudunmawar bawa kungiyar Fom din koyar da sana’a har guda goma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: