An kama sarkin Wakar Sarkin Kano
Yawaitar kama mawaka da sauran yan adawa ya fara kaiwa intaha Kano, yanzu nan, aka je har gidan Nazir Sarkin wakar sarkin Kano,aka kama shi kuma a je neman beli ance sai dai gobe a dawo, a kwanakin baya an kama Oscar, haka kuma rahotanni na cewar akwai mutanen da aka lissafa ake kamasu daya Bayan daya, saboda wakokin su, sun Mara Bayan akidar Kwankwasiya. Kamun farko Sadeek Zazzabi aka fara kamawa aka kuma kaishi kurku, daga bisani aka kama Sunusi Ocar 442,yanzu gashi an kama sarkin Wakar Sarkin Kano. Abin tambayar shine, meye laifinsu,. A baya dai an lissafa wasu mawaka wadanda aka ce suma duk daya Bayan daya sai kamasu. Abin dake ban mamaki shine wacce doka suka karya Rarara Bai karya ta, Kuma Ana kama su ne saboda a birge lamba daya ko kuma tsabar neman gindin zama ne yake Sawa wasu suna fin Mai Kora shafawa? Ina Bawa Mai girma Gwamna shawara da ya Sanya idanu kan masu son birgewa ta hanyar taka mutane irin wadannan Bama kaunar gwamnan suke ba, suna amfani da dama ne domin wata biyan bukata tasu.

Nasiru Salisu Zango

