Instagram: Wacece Jakadiyyan Tona Asiri?

Jakadiyyan Tona Asiri wani asusu ne a dandalin sada zumunta na Instagram wanda yayi suna wajen bin diddigi da tone-tone, shafin Jakadiyya ya maida hankali wajen ragargaza akan jaruman fina-finan Hausa wato Kanny Wood sai kuma wasu daga jaruman Social Media.
Jakadiyya tana da asusu kala-kala sama da guda a shafin na Instagram.

Jaruma ta soki jarumai irinsu Maryam Yahya, Sadiya Kabala, Teema Makamashi, Umma Shehu da sauransu.

Jakadiyyar tasha jifan tsagin wasu daga ciki da cewar suna aikata dabi’ar nan ta neman mata, ko kuma ta jefi wasu da karuwanci, haka abin yake a bangaren sauran jarumai da suke taka leda a shafukan social media, domin kuwa an sha tafka dambarwa tsakanin Jaaruma Empire, Muneerat Abdussalam, Sadiya Haruna da kuma Mariya Balan Kundi da sauransu.
Ra’ayin al’umma ya rabu akan abubuwan da Jakadiyya keyi yayinda wasu ke kallon abinda ta keyi a matsayin aikin alheri ko kuma fadar gaskiya, wasu kuma na kallon abinda take yi a matsayin cin zarafi da kuma cutarwa ga wadanda take batu akansu.
Duk da wannan dambarwa da ake sai dai wani abun mamaki shine babu wanda ya san ko wacece wannan Jakadiyyar.
Shin Ko Wacece Jakadiyya?
Masu bibiyar shafin Jakadiyya suna siffanta ta a matsayin matashiyar Budurwa wadda ke cikin duniyar Kanny Wood wadda ta san sirrinsu kuma take bibiyarsu, sannan ma’abociyar social media, hakan yasa take iya samun rahotonni akan lokaci.
Sai dai masana da kuma masu nazartar al’amuran dake faruwa a social media na kallon Jakadiyya cewa wani mutum ne wanda ya riga ya san harkar social media sannan yake cikin duniyar Kanny Wood yake amfani da damarsa ya samar da asusun, domin kuwa abubuwan da Jakadiyyar keyi na nuna cewa abubuwan da take yi abune da tilas sai mai ilimin social media ne zai iya yi, ba wai gama gari ba.
A Sharhi na gaba, in Allah ya yarda zamu kalli wasu daga ayyukan da Jakadiyyar ke aiwatarwa domin yin tsokaci akai.
Mujallar Matashiya
11-09-2019.