Connect with us

Labaran jiha

Instagram: Wacece Jakadiyyan Tona Asiri?

Published

on

Jakadiyyan Tona Asiri

Instagram: Wacece Jakadiyyan Tona Asiri?

Jakadiyyan Tona Asiri wani asusu ne a dandalin sada zumunta na Instagram wanda yayi suna wajen bin diddigi da tone-tone, shafin Jakadiyya ya maida hankali wajen ragargaza akan jaruman fina-finan Hausa wato Kanny Wood sai kuma wasu daga jaruman Social Media.

Jakadiyya tana da asusu kala-kala sama da guda a shafin na Instagram.

Jaruma ta soki jarumai irinsu Maryam Yahya, Sadiya Kabala, Teema Makamashi, Umma Shehu da sauransu.

Jakadiyyar tasha jifan tsagin wasu daga ciki da cewar suna aikata dabi’ar nan ta neman mata, ko kuma ta jefi wasu da karuwanci, haka abin yake a bangaren sauran jarumai da suke taka leda a shafukan social media, domin kuwa an sha tafka dambarwa tsakanin Jaaruma Empire, Muneerat Abdussalam, Sadiya Haruna da kuma Mariya Balan Kundi da sauransu.

Ra’ayin al’umma ya rabu akan abubuwan da Jakadiyya keyi yayinda wasu ke kallon abinda ta keyi a matsayin aikin alheri ko kuma fadar gaskiya, wasu kuma na kallon abinda take yi a matsayin cin zarafi da kuma cutarwa ga wadanda take batu akansu.

Duk da wannan dambarwa da ake sai dai wani abun mamaki shine babu wanda ya san ko wacece wannan Jakadiyyar.

 

Shin Ko Wacece Jakadiyya?

Masu bibiyar shafin Jakadiyya suna siffanta ta a matsayin matashiyar Budurwa wadda ke cikin duniyar Kanny Wood wadda ta san sirrinsu kuma take bibiyarsu, sannan ma’abociyar social media, hakan yasa take iya samun rahotonni akan lokaci.

Sai dai masana da kuma masu nazartar al’amuran dake faruwa a social media na kallon Jakadiyya cewa wani mutum ne wanda ya riga ya san harkar social media sannan yake cikin duniyar Kanny Wood yake amfani da damarsa ya samar da asusun, domin kuwa abubuwan da Jakadiyyar keyi na nuna cewa abubuwan da take yi abune da tilas sai mai ilimin social media ne zai iya yi, ba wai gama gari ba.

A Sharhi na gaba, in Allah ya yarda zamu kalli wasu daga ayyukan da Jakadiyyar ke aiwatarwa domin yin tsokaci akai.

 

Mujallar Matashiya

11-09-2019.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Wata Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Yunkurin Sayar Da ‘Yarsa A Jihar Legas

Published

on

Wata babbar kotu da ke Jihar Benue ta bayar da izinin garkame wani mutum wanda yayi kokarin sayar da ‘yarsa akan kudi Naira Miliyan 20.

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar su ne wadanda su ka gurfanar da wanda ake zargin shi da abokinsa a gaban kotun.

Jami’an sun ce abokin nasa shine wanda ya taimaka masa wajen hadin baki domin a siyar da yarinyar da kuma safarar mutane.

Jami’ar ‘yar sanda mai gabatar da kara ta bayyana cewa an kama mutanen ne a lokacin da su ke kokarin sayar da yariyar mai shekara hudu.

Ta ce ana tsaka da cinikin yarinyar su ka kama mutanen yayin da mutumin da za su sayarwa da yariyar ya tsere.

Jami’ar ta kuma bukaci kotun da ta yanke musu hukuncin sakamakon karya wasu dokokin da su ka saba dokar Jihar.

Bayan gabatar da karar Alkaliyar kotun ta aike da su gidan yari zuwa ranar daya ga watan Disamba domin ci gaba da da shari’ar.

Continue Reading

Labaran jiha

‘Yan Sanda A Jihar Legas Sun Tsinci Wani Jajiri A Cikin Leda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da tsintar wani jajiri wanda ake kyautata zaton mahaifiyarsa ce ta jefar da shi a cikin Kwandon shara.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Benjamin Hundeyin ya ce an tsinci yaron da aka jefar ne a cikin Leda.

Kakakin wanda ya dora hoton jajirin a shafinsa na Twitter a jiya Alhamis ya ce ba don an yi gaggawar gano yaron ba da tuni ya rasa ransa.

Benjamin ya kara da cewa tun bayan tsintar yaron yana cikin koshin lafiya.

Kakakin ya yi kira ga mata masu dabi’ar zubar da ciki da su daina hakan don ya saɓa da dojar ƙasa.

Inda ya ce jefar da jajiran babban laifi ne kuma idan aka kama mutum zai fuskanci hukuncin mai tsanani.

Continue Reading

Labaran jiha

‘Yan Bindiga Sun Karbi Buhun Shinkafa 20 Da Kayayyaki A Matsayin Kudin Fansa

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun saki wasu mutane 12 da su ka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

Kafin sako mutanen ‘yan bindigan sun karbi buhun shinkafa 20 da buhun Wake 20 jarkar Man gyada Jarkar Manja da kuma katin waya harna naira 10,000 a matsayin fansar mutanen da su ka sace.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun hallaka wani Manomi tare da yin garkuwa da mutane 20 a cikin gonakinsu da ke yankin Jangali da kwada duk da ke cikin yankin na Birnin gwari.

Kungiyar ci gaban masarautun Birnin Gwari BEPU ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugaban kungiyar Ishak Usman Kasai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce a baya ‘yan bindigan sun nemi naira 12 a matsayin kudin Fansar wasu manoma da su ka yi garkuwa dasu.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: