Shugaban kasa Muhammad Buhari yace babu ragowar yan kungiyar Boko Haram a kasar nan face Wasu tsirarun yan bindiga a Arewa maso gabashin kasar nan.

Shugaban kasa ya bayyana hakan nee lokacin da yake karbar bakoncin Yan kungiyar ICRC a fadarsa dake abuja a jiya.
A cewar Shugaban kasar An ruguza kungiyar Boko Haram Amma har yanzu akwai ragowar mambobinsu Wanda ke Kai hare hare a gabar Tafkin chadi.

Muhammad Buhari yace wanann Dalilin yasa suke gudanar da aikin hadin gwaiwa da Kasashen dake makwafta da Najeriaya, Wanda suka hada da chadi, kamaru, sai jamhuriyar Nijer don Ganin an fatattakesu baki daya a duniya.

Rfi