Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi nasarar kwato shanu sama da dubu tare da kama mutum uku da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Ahmed Ilyasu ne ya shaida hakan ga manema labarai a kwanar ɗangora jim kaɗan bayan ka`ala aikin ceto shanun.
Ya ce an kwace manyan makamai daga hannun masu satar mutanen tare da kayan soji da kuma alburushi mai tarin yawa.
Cikin nasarar da rundunar ke samu duk mako a wannan karon rundunar ta haɗa kai da ƙungiyar miyetti Allah wanda suka bada gudunmawa wajen samun nasara a cikin dajin.
Kalli hotunan da ke ƙasa