Jami’an tsaron masu yaki da yan fashi Ta SARS sunyi awon gaba da wani matashi mai suna Bashir Bashir Galadanci dake magana da yawun tsohon kakakin Rundunar yansandan jihar Kano SP magaji Musa majia. A shafin sada zumunta na Facebook.
Rundunar sun cafke shine bisa zargin yarfe da bata suna ga kakakin Rundunar na yanzu ASP Abdllahi Haruna Kiyawa.
Da yake jawabi akan kama matashin Abdullahi Kiyawa yace bashi da masaniya game da kama matashin da sunan yana masa yarfe.
Sai dai yace Yana yin yarfe ne da hukumar yansanda baki daya ba wai shi kadai ba.
Bashir Galadanci dai yayi kaurin suna a shafin sada zumunta wajen yada manufofin tsohon kakakin Rundunar yansandan jihar Kano SP magaji Musa majia wanda aka sauya masa aiki zuwa jihar jigawa.