Gwamnatin jihar kaduna zata yi dokar da zai hana likitan dake aiki a asibitin gwamnati kuma ya dinga aiki a asibiti mai zaman kansa ba a jihar.

Gwamnatin tace zata aike da kudurin Majalisar dokoki don Tattaunawa tare da tabbatar da dokan hana likitoci aiki a asibitoci guda biyu a jihar.
Gwamnan jihar malam Nasir El- Rufa’i ne ya bayyana hakan a lokacin da ake hira dashi a wata kafar yada labarai a jihar.
Inda yace gwamnatinsa bazata lamunci wannan hali duk da yasan al albashin gwamnati ba zai ishesu ba.
Amma dole ne su mai da hankali kan aikin da aka daukesu.

