Ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa reshen jihar Kano sun buƙaci haɗin gwiwar ƴan sanda a kan masu kuste cikin aikin jarida.
Shugaban ƙungiyar Mallam Abbas Ibrahim ne ya nemi hakan yayin da suka kai ziyara ofishin kwamishinan ƴan sandan jihar kano Ahmed Ilyasu.
Ya ce akwai masu kutse da sunan aikin jarida wanda ba su san ko bihim a aikin ba, kuma suna taka rawa wajen gurɓata aikin tare da rage ƙimarsa a idon al umma.
Abbar Ibrahim ya roƙi haɗin kan jami an ƴan aandan jihar Kano don ganin an kawar da bara gurbi masu ƴaɗa labaran ƙarya musamman a kafafen sada zumunta.
A nasa ɓangaren kwamiahinan ƴan sandan jihar Kano Ahmed Ilyasu ya tabbatar da cewa, rundunar a shirye ta ke na ganin an kawar da dukkan ɗabi ar da ta kasance haramtaciyya a cikin doka, sannan ya yabawa ƴan jaridu ganin yadda suke aiki ba dare ba rana don yaɗa ayyukan ƴan sanda.