Hukumar yaki da masu yiwa Tattalin Arziki zagon kasa ta EFCC tace sun samu korafe korafe na badakalar kudade kan tsofaffin gwamnoni biyu,
Eng Dr Rabi’u Musa kwankwaso na kano da Aliyu magatakaddar wammako na sokoto, bisa zargin su da sarrafa kudade ba ta yadda yakamata ba lokacin da suke gwamnoni.

Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujure shine ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust.

Inda yace hukumar tana zargin kwankwaso ne da juya akalar Kudaden kananan hukumomi 44 kimanin Naira biliyan 4.

Shikuma wammako ana zargin sa ne da sama da fadi da Kudaden Al’umma har naira Biliyan 15.

Wani Mai suna Mustapha Danjuma shine shine ya Mika koken ga Hukumar EFCC a madadin Abubkar Mai sha’ani da Alhaji Najumai Kobo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: