Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ta yabawa gwamnan jihar Kaduna malam Nasir El-Rufa’i kan matakin da ya dauka na Kin Rushe tsohon cocin Anglican dake garin Zaria.

A cewar Shugaban kungiyar CAN Reshen jihar Kaduna Rev Joseph Hayab yace cocin yakai shekaru 110.
Yace dole ne a yaba wa gwamnan jihar kaduna.

Shima anasa jawabin Babban Daraktan hukumar cigaba da tsara birane Ismail Dikko yace baza’a taba cocin ba don ya shiga hanya saboda tsohon coci ne na tarihi, amma zai Kasance yadda yake, sai dai za’a tashi kasuwannin da suke kewaye da wurin. Don ganin an samu hanya mai fadi

Leave a Reply

%d bloggers like this: