Babban malami mai wa azi da sulhu a hukumar Hizbah Shek Muhammad Tukur Moriki Rijiyar Lemo ne ya bayyana hakan ta cikin wani shiri na Rabin Ilimi.

Malamin ya da wanda ya zuƙin tabar wiwi da wanda ya kwankwaɗi kwalbar giya wato barasa hukuncinsu ɗaya a musulunci.
Malamin ya ƙara da cewa, kamar yadda giya ke saka maye haka ma tabar wiwi na saka maye kuma dukkan abinda zai sa maye dai dai yake da giya.

Haka kuma ya ja hankali ga masu zuƙar taba sigari da cewa a musulunce babu nassi ko aya da ta halatta shan taba sigari, haramun ne baki ɗaya.

A taƙaice dai idan mutum ya sha tabar wiwi za a masa bulala ɗari kamar yadda za a yiwa wanda ya sha giya.