Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a JAMB ta fitar da sanarwar cewa duk wani dalibi mai son yin rijistar jarabawar dole sai ya mallaki katin shaidar dan kasa.

Kakakin hukumar Fabian Benjamin ni ya bayyana hakan a jiya,.
Inda yace wannan sabon Shirin zai taimaka wajen magance magudin jarabawa, kasancewar katin shaidar dan kasa yana dauke da bayanan yatsun hannun Mutum da sauran Cikakkun bayanai.

Benjamin ya shawarci dalibai dake Shirin rubuta jarabawar UTME dasu tabbatar sun mallaki katin shaidar dan kasa.
