Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana iya kokarinta don ganin ta inganta Rayuwar Al’ummar kasar Nan.
Sakataren gwamnatin Tarayyar kasar Nan Boss Mustapha shine ya bayyana hakan ga manema labarai, a lokacin da yake gabatar da bayanan irin shirye shiryen da ofishinsa ke yi kan bikin zagayowar murnar Samun yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka yau shekaru 59 kenan.
A cewar Boss ana murna ne da zagayowar ranar yanci amma a zahiri ana bakinciki ne kasancewar yadda kasar Nan ke fuskantar ta koma baya na rashin cigaba.
Duk da irin kokarin da Shugabannin baya sukayi amma an kasa samun cigaba.
A cewar sa Shugaban kasa Muhammad Buhari ya daura dambar kawo sauye sauye a kasarnan don ganin an inganta Rayuwar Al’ummar kasar nan.