Jarumi Adam Zango ya ƙaryata Wani malami da ya zargi jarumi Adam Zango da neman mata ƴan ƙasa da shekaru 20.
Malamin ya yi wannan magana ce a masallaci inda ya zargi jarumin da neman mata ƴan ƙasa da shekaru 20 da zummar sakasu a wani sabon fim ɗinsa mai suna SABON SARKI.
Malamin ya ce masana antar na shirin tsaftace sana ar kuma a dalilin ƙin bin tsarin addini da al ada ne ya sa jarumin ya fice daga masana antar.
Adam Zango ya musanta wannan zargi inda ya fito a wani faifan bidiyo ɗauke daAlƙur ani yana mai rantsuwa da Allah cewa malamin ƙarya ya ke masa.
Haka kuma Adam Zango ya ce ya fito ne don kare kansa gudun barin iyalinsa da tabo.
Sannan ya roƙi sauran malamai da su ja kunnen malamin ganin cewa ba shi da hujja a bisa zargin da yake masa.
Sannan ya ce ya bar masana antar ne bisa rashin adalci da ake yi masa, kuma ɗaukakarsa ce ta sa ake ta masa bita da ƙulli.