Babbar kotun karɓar ƙorafin zaɓe a Kano ta saka ranar laraba 2 ga watan Oktoba mai kamawa a matsayin ranar da za ta yi hukuncin ƙarshe a kan shari ar.

Hakan ya biyo bayan karɓar dukkanin shaidu daga kowanne ɓangare ciki har da hukumar zaɓe mai zaman kanta wato INEC.
Jam iyyar PDP ta kai ƙarar kan zaɓen gwamna da aka yi wanda ke ƙalubalanta da cewa ba a yi adalci ba wajen bayyana cewa Abdullahi umar Ganduje ne ya lashe zaɓen

