Jarumin ya bayyana cewa yana yin sana ar ne saboda ita ya iya kuma idan ya samu wata a shirye yake ya bar wasan hausa, a cewarsa, ba yana yi ne don birgewa ba illa sana ar da yake samun taro da sisi.

“Kuma a shirye nake na bar wannan sana ar matuƙar na samu wata” inji jarumin.
Duka dai cikin martanin da yake na cewar mahassada sun yi masa yawa har ake masa ƙazafi saboda ɗaukakar da Allah ya masa, jarumin ya yi wannan furuci ne cikin martanin da ya yiwa wani malami da ya zageshi da cewa yana neman mata.

Jarumin ya ce ba wata hujja da malamin zai iya kawowa kuma ba zai kaishi kotu ba saboda malamin na yin rigima da shi ne aboda ya yi suna.

Idan ba a manta ba, a baya bayan ne wani malami ya zagi jarumin da neman mata tare da ɓata tarbiyya lamarin da ya saya fice daga ƙungiyar masana antar masu shirya fina finai ta Kannywood.
Lamarin da jarumin yace sam ba haka abin yake ba.