Firaiministan Ingila Boris Johnson yana cigaba da matsa kaimi kan kungiyar Tarayyar turai cewa kasarsa ta shirya ficewa daga kungiyar Tarayyar, ko da Yarjejeniyar ko babu.
Johnson yace kasar zata fice ne a ranar 31 ga watan da muke ciki.
Mr Johnson ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron shekara shekara na Jam’iyarsa masu masu tattsauran Ra’ayi a garin Manchester.
Ya kara da cewa Birtaniya na da hanyoyin samun mafita da za su dogara da kansu ba tare da samun tallafin daga kungiyar Nahiyar Turai.
Priministan dai na fuskanta kalubale tun da ayyana ficewa daga kungiyar Tarayyar Nahiyar Turai.