Wannan shi ne karo na bakwai da Mujallar ke ƙoƙarin bada horon sana o i ga matasa kyauta.
Mujallar Matashiya dai ta shahara wajen bada horon sana kyauta ga matasa, tare da ƙoƙarin saka matasan a hanya ɗon ganin sun cigaba da ririta abinda suka koya.
A baya ma mujallar ta yi makamancin wannan wanda ta horas da matasa fiye da dubu ɗaya ciki Kano da sauran jihohi.
Cikin sana o in da kamfanin yaɗa labaran ya ɗauki nauyin horas da su akwai ɗaukar hoto mara motsi, da hotuna masu.motsi, sarƙa da ɗan kunne, gyaran janareta, kwalliya da sauransu.
A tarohi wannan ne kamfanin yaɗa labarai mai zaman kansa da yayi wannan hoɓɓasa don rage yawan masu zaman kashe wamdo a jihar kano da ma faɗin Najeriya.
Ana sa ran cigaba da bada wannan horo nan ba da jimawa ba.