Kwanaki ƙaɗan bayan da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasara a kotu har ma shugaban Ƙƙsa Muhammadu Buhari ya tayashi murna, suma haɗaɗɗun jam iyyun ma suka marawa APC baya tare da manyan ƙungiyoyi sun aike da saƙon taya murmarsu ga gwamnan Kano Abdullahi Ganduje bisa nasarar da ya samu a kotu.

Cikin wata takarda da shuggabannin ɓangarorin biyu suka aike ga gwamna Ganduje ɗauke da sa hannun Cif Benjamin Aturu Dogo da Bello Sanin Kwalla, sun taya gwamnan murma tare da jinjinawa bisa bin umarnin kotu har ya kai ga nasara.

Fiye da jam iyyu 50 ne ke ƙarƙashin wannan ƙungiya sannan kuma da wasu ƙungiyoyi daban da suka marawa gwamna Abdullahi Ganduje baya a zaɓen 2019.

Takardar na ɗauke da jaddada goyon baya ga mulkin gwamna Ganduje inda suka sha alwashin aiki tare don ɗaga darajar jihar kamar yadda suka bayyana.

Idan ba a manta ba ɗan takarar jam iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ne ya kai ƙara kotun sauraren ƙorafe ƙorafen zaɓe inda yake ƙalubalantar nasarar Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma kotu ta tabbatar da nasararsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: