Kasar Amurka tayi Alkawarin bayar da Dala Miliyan 5 ga duk Wanda ya taimaka mata da bayanai kan Shugaban kungiyar IS a Yankin Afrika da yayi ikirarin Kashe dakarun Amurka da na Nijar shekaru biyu da Suka gabata.
Amurka na neman Walid Al-Sahrawi ne tun bayan da ya dauki alhakin farmakin da mayakan IS Suka kaiwa sojojin Amurka da Nijar a kauyen Tongo-Tongo ranar 4 ga watan Oktoban 2017, inda Suka Hallaka sojojin Amurka 4 da na Nijar 5.
Tun bayan Kai farmaki tun wancan lokacin har yanzu babu wanda aka kama dake da alaka da harin na Tongo-Tongo don haka Amurka ta fitar da sanarwar biyan Dala Miliyan 5 ga Wanda ya bada jawabin sirrin kungiyar IS.