Gwamnatin jihar jigawa ta amince zata fara biyan sabon tsarin Albashi mafi karanci dubu 30.

Mai Rikon mukamin Shugaban ma’akantan jihar Alhaji Hussain Ali Kila shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya.

A cewar Hussein Kila gwamnatin jigawa ta amince zata fara biyan sabon tsarin Albashi ga ma’akata a karshen watan oktoban nan.

Ya kuma ce a ranar 8 ga watan Oktoban ne gwamnati zata tattauna da kungiyar kwadago ta jihar don cimma matsaya akan fara biyan sabon tsarin Albashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: