Hukumar Tattara haraji ta jihar Kaduna ta rufe wasu sassan Bankunan Access na jihar Sakamakon Rashin Biyan Haraji da suka ki biya.

Hukumar dai na bin bankunan bashin naira Miliyan 175.

Sakataren Hukumar kuma Mai bada shawara akan shari’a Francis Kozah shine ya shaid hakan ga manema labarai inda yace bankunan zasu Kasance a rufe har sai sun biya bashin da ake binsu.

Kamfanin dillancin labarai ta kasa ta rawaito cewa bankunan Access dake Rufe a jihar Kaduna sun hada da na Titin Bida, da na Titin Ahmadu Bello, sai kuma Titin isa Kaita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: